Talauci ko Neman Sauƙi: Rahoto ya nuna ƙaruwar sayen Tsofaffin wayoyin iPhone, Samsung da Kashi 10 a Najeriya
Adadin mutane dake sayen tsofaffin wayoyin iPhone da Samsung a Najeriya yakai kashi 10 a Shekarar 2021, kamar yadda Hukumar Bincike kan Kasuwa ta Bayyana.
A cewar Hukumar Kula Binciken ta Duniya, a shekarar 2021 an samu ƙaruwar sayen iPhone inda yakai kashi 15.
KARANTA WANNAN LABARIN: DA DUMI-DUMI: ‘Yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin yakin neman zaben gwamnan Osun, sun jikkata yan jarida
Tace har yanzu farashin wannan kaya ya zamanto ma yawa, wanda shiyasa da yawa daga cikin masu sayen kayayyakin suke neman Tsofaffi na wayoyin Apple da Samsung. Ta ƙara dacewa wayoyin Apple sune akafi neman tsofaffi a Kasuwanni.
Wani masani Glen Cardoza yace “tsofaffin wayoyi wani ɓangare ne yadda kasuwar su ke ci, kuma suke cigaba da karaɗe ko’ina.
“Kasuwancin Tsofaffin wayoyi sune abinda yake cigaba da yawaita ta fuskar nema, yanayin yakai kashi ƙaruwar da kashi 10 a Shekarar 2021. Muna ganin neman wadannan Shekara zuwa Shekara musamman a kasuwannin China, da India, da Latin Amurka, yankin Kudu maso Gabas na Kasar Asia, da Kuma Afirka.
A cewar Hukumar Binciken Amerika da Indiya sune Ƙasashen da suka fi ko’ina neman tsofaffin wayoyin da kashi 29 zuwa 25.
Amma kuma Ƙasar Amurka da China da Europe sune suka neman wayoyin a Shekarar 2020.
A wani rahoto na Shekarar 2020 da Kamfanin Apple ya fitar kashi 6. 41 na ƴan Najeriya ne ke amfani da wayoyin ta.
Comments 1