Mujallar The Economist wadda ake bugawa a Burtaniya, ta ce ‘yan Najeriya sun kara fadawa yanayin kangin talauci a wa’adin mulkin Shugaba Buhari na farko.
A bugunta na ranar 30 ga watan Mayu, mujallar ta bayyana tattalin arzikin kasar da wanda ya “tsaya cak tamkar babbar motar da ta makale”.
The Economist ta kara da cewa samun kudade da ‘yan kasar ke yi ya yi “kasa warwas” a shekaru hudun da Shugaba Buhari ya kwashe yana mulki.
Ta kuma ce ko da Hukumar ba da Lamuni ta Duniya, IMF ba ta tsammanin ‘yan kasar za su murmure a shekaru shida masu zuwa.
Sai dai gwamnatin Buhari ba ta ce komai ba kan rahoton mujallar. Amma a baya gwamnati ta dora alhakin tabarbarewar al’amura a kasar a kan gwamnatocin da suka gabace ta.
Wasu alkaluma da mujallar ta fitar sun nuna cewa rashin aikin yi tsakanin ‘yan kasar ya kai kaso 23 cikin 100, sannan kuma hauhawar farashi ya daga da kashi 11 cikin 100.
Har wa yau, The Economist ta kara da cewa ‘yan Najeriya miliyan 94 ne ke rayuwa karkashin samun da ya gaza dala 1.90, kwatankwacin naira 684 a duk rana.
Hakan na nuni da cewa a Najeriyar ne kadai a fadin duniya samun ‘yan kasar ya gaza dala biyu kuma abin karuwa yake yi a kullum.
Wani abin takaici da mujallar ta The Economist ta hasaso shi ne yadda a shekarar 2030 za a samu yiwuwar samun dan Najeriya daya a kowane mutum hudu matalauta a duniya.
To sai dai mujallar ta ce duk da cewa tun kafin hawan Shugaba Buhari karagar mulki a shekarar 2015 tattalin arzikin kasar ya dauki hanyar sukurkucewa, amma ‘yan kasar “sun fi jin jiki” a zamanin shugaban.
Masana harkar tattalin arziki na Najeriya ba su karyata bincike da alkaluman da mujallar ta The Economist ta fitar ba.
Bilhasali ma sun kara fito da batutuwan da jaridar ta ambata a fili. Sai dai sun yi wa shugaba Buharin uzuri a wasu fannoni.
Abubakar Aliyu wani masanin tattalin arziki a Abuja, Najeriya ya ce “A saninmu gwamnatin Buhari ta kashe makudan kudade kimanin naira tiriliyan hudu a shekaru ukun da suka gabata wajen ayyukan raya kasa kamar shimfida titunan mota da na layin dogo”.
Sai dai ya ce “karfin tattalin arzikin Najeriya nan da shekaru masu zuwa ya dogara ne kacokan kan fito da tsare-tsare da kuma samun mutanen da za su taimaka wa shugaban zartar da su, to babu wani abu da gwamnatin za ta tabuka’.
Arewa tafi kudu talauci
Dr Zahumnam Dapel, wani masanin tattalin arziki a Najeriya, ya ce arewacin kasar ya fi kudanci fama da matsanancin talauci ne saboda ba ya sa samun kudin shigar da ya kai na kudu.
Dr Zahumnam wanda ya shaida wa Wakilinmu hakan a watan Satumbar 2018 ya kara da cewa “kudaden shigar da jihohin Legas da Ribas suke samu a shekara sun fi wadanda jihohi 14 na arewacin kasar ke samu, don haka suna da damar da za su kashe su kan al’umominsu.”
Masanin tattalin arzikin, wanda ya yi aiki a Amurka, ya kara da cewa yawan talakawa da ke ci gaba da haihuwa ba tare da samun abin da za su bai wa iyalansu ba a arewacin Najeriya ya taimaka wajen ta’azzara talaucin da yankin ke ciki.