Mai Magana da yawun Taliban Suhail Shaheen a yau Talata ya bayyana cewa, Kungiyar Taliban ba ta da wani yunkuri na sanya wasu takunkumin daka’iya haramta amfani da kafafen sadarwa na zamani a kasar Afghanistan.
Shaheen ya Kara da cewa, Taliban ta yi amanna da yancin fadin albarkacin baki, Kuma a shirye take ta amshi kalubalantar al’uma, sai dai ya ce, Kungiyar za’a ta sanya Ido wajan rage yada labarin karya a fadin kasar.
Mai Magana da yawun Taliban din ya ce, “Sam babu wani batu kan kakaba takunkumin a kafar sadarwa na zamani, domin mun yi Imani da yancin fadin albarkacin baki”
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta aike da wani Dan kasuwa Gidan yari a Legas
“Don haka, Mutum zai iya kalubalantar aiyukan mu, ko kuma bayyana wasu manufofin shi, tabbas abu ne Mai kyau, domin duk suna daya daga cikin yancin fadin albarkacin baki” inji shi.
“Amma abun da baza mu lamunta ba shi ne, yada karai-rayi, da kuma labaran Kanzon kurege, wadanda tabbas za mu kula da su matuka” a cewar Shaheen.
A wani labarin Kuma na daban.
Yan bindiga sun harbe Yan kungiyar Sakai biyu har lahira, a wani musayan wuta da ya afku tsakanin bangarorin biyu a garin Mayaki dake karamar hukumar Lapai na jihar Niger.
Garin Mayaki ya yi iyaka da yankin Gwaje na babban birnin tarayya Abuja.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, lamarin ya afku ne a ranar Lahadin data gabata, da musalin karfe 10:23 na safe, inda wasu Yan bindiga su kayi wa jami’an Sakai kwantan bauna.
Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunan shi a mastayin Amadu ya ce, Yan kungiyar sakan sun mai dawa Yan bindigan wuta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mambobin sakan biyu.
Kwamandan jami’an Sakai na jihar Niger reshen karamar hukumar Lapai Muhammadu Ibrahim ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Inda ya ce, “Tabbas gaskiya ne, mun rasa biyu daga cikin jami’an mu, a wani harin kwantan bauna a dajin Mayaki, ya yin da jami’an muke sintiri” inji shi.
” Kuma a Yanzu da muke magana da ku, mun sanar da jami’an dake yankin da su ci gaba da farmakan yan bindigan” a cewar shi.
Sai dai a nashi bangaren, Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Niger ASP Wasiu Abiodun, bai dauki waya ba, kuma bai amsa sakon kartak kwana ba, da manema labarai suka tura ma shi.
Comments 1