A yau Asabar, an haramta wa yan mata komawa makarantun sakandare a Afghanistan, bayan sabbin shugabannin Taliban na kasar sun ba da umarnin samari da malamai maza ne kawai za su koma aji domin karatu.
Kungiyar masu tsatsauran ra’ayin Islama ta kori gwamnatin da Amurka ke marawa baya a watan da ya gabata, inda ta yi alkawarin yin mulki mai sassauci fiye da mulkinsu na tsatstsauran ra’ayi a shekarun 1990, lokacin da aka haramta wa mata yawan karatu da aiki.
Amma sabon sanarwar da ta fito daga ma’aikatar ilimin kasar, ta kasan ce sabon yunƙurin daga sabuwar gwamnati na Taliban, na yin barazana ga tauye hakkokin hakkin mata.
Sanarwar ta ce “Duk malamai maza da ɗalibai ya kamata su halarci Makarantun su,” inji wata sanarwa daga Taliban, kafin fara karatun a yau Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Shugaban Algeria Abdelaziz Butefileka
Sanarwar, wacce aka fitar da ita cikin daren jiya Juma’a, ba ta lamunce wa malamai ko dalibai mata koma wa makarantu ba.
Sai dai idan za’a iya tunawa tun bayan barkewar cutar Corona a kasar, Makarantun sakandare, da suka kunshi dalibai masu shekaru tsakanin 13 zuwa 18, galibi ana rarrabe su bisa dubi da jinsi a Afghanistan.
Comments 1