By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Talata ne kungiyar Taliban ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da wani kamfani mai cibiya a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) kan kula da filayen jiragen sama guda uku a Afganistan.
Da sabuwar yarjejeniyar, sabbin jami’ai a Kabul da wakilin kamfanin UAE ta kafa na fatan dukkan kamfanonin jiragen sama na kasuwanci na kasa da kasa za su iya dawowa da zirga-zirgar jiragensu zuwa kasar.
“Kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa, sun yi nesa da kasar nan tsawon watannin da suka gabata.
“Muna fatan za su dawo gare mu,” in ji babban darektan Kamfanin GAAC na UAE, Razack Aslam.
Kasashen Qatar da Turkiyya sun shafe watanni biyu suna tattaunawa da jami’an Taliban don tafiyar da filayen jiragen saman kasar.
Sabuwar yarjejeniyar da aka kulla da Hadaddiyar Daular Larabawa za ta shafi kayan aiki ne kawai a filayen jirgin saman Kabul, Herat da Kandahar amma ba tsaro ba.
“Wannan kwangilar ta hada da wani bangare na ayyukan,” in ji mataimakin ministan sufuri da zirga-zirgar jiragen sama na Taliban.
“Har yanzu muna fatan ci gaba da tattaunawa da Qatar kan wasu sassa biyu da suka hada da tsaron jiragen sama, kamar bincike da duba fasinjoji da kuma kula da zirga-zirgar jiragen sama.”
A halin yanzu an rufe sararin samaniyar Afganistan ga duk wani tashin jiragen sama.
Jiragen cikin gida da na yin ƙaura ko na isar da agajin jin kai ne kawai ke gudana.
NAN
Comments 1