Hukumar NEMA ta rarraba kayan tallafin wadanda suka hada da abinci da sauran kayayyaki daban-daban ga mutane 4,000 da iftila’in ambaliya ya rutsa dasu a Jalingo Jahar Taraba.
Ambaliyar ta shafe gidaje kimanin dari biyar da gonaki da dama. Kamar yadda Jaridar Vanguard ta wallafa a shafinta
Alhaji Mustapha Habib, shugaban Hukumar ta NEMA a lokacin da yake rarraba kayan tallafin cewa yayi, anyi hakane don rage radadin kan wadanda abun ya shafa.
KARANTA:- YANZU-YANZU: Hukumar NAFDAC ta amince da wasu sabbin Magungunan cutar Covid-19
Sai dai Mista Alli Kadiri shugaban Hukumar NEMA reshen Jahar Yola shine ya wakilci Alhaji Mustapha Habib.
Yace da yiwuwar karo masu kayan tallafin bayan kammala binciken adadin barna da ambaliyar ya janyo.
Yace tallafin ya hada da na hukumar Jinkai ta Kasa, wadda Sadiya Faruk Umar ke jagoranta, inda ta bada umarin bada kayan tallafin 21 wanda suka hada da abinci da sauran kayayyaki daban-daban.
Alhaji Mustapha Habib ya kara kiraga Mutanen Jalingo da su daina gina gidaje a kan hanyar ruwa.
Daya daga cikin wadanda iftila’in ya rutsa dasu Mista David Said, ya yabama gwamnatin tarayya kan kokarin rarraba masu kayan tallafin da tayi.
Said yace wannan ya nuna mana cewar gwamnatin tarayya Najeriya bata manta damu ba, Kuma yasa ya tabbatar masu da su Yan Najeriya ne.
Kamar yadda yace kayan tallafin zai rage masa radadin na tsawon lokaci.
Ya Kuma roki gwamnati data agazama Mutanen wanda abun ya rutsa dasu data taimaka musu da kayan gini don sabunta gidajen su.
A wani labarin
Gobara: NEMA ta raba Kayan Tallafi ga Yan Kasuwar Katsina Da Iftila’in ya shafa.
Hukumar Bayarda Agajin Gaugawa ta Kasa ta rarraba kayan tallafi ga yan kasuwa da lamarin gobara ya shafa a babbar Kasuwa ta Katsina.
Gwamna Aminu Bello Masari ne ya kaddamar da rarraba kayan tallafin a farfajiyar kasuwar.
Kayayyakinda aka rarraba sun hada da buhunan shinkafa, da na wake, da sukari, da man girki, da katan-katan na madara gami da magi da dai sauransu.
Da yake kaddamar da raba kayayyakin,Gwamna Masari wanda Kwamishinan Wasanni da Walwalar Jama’a Alhaji Sani Aliyu Danlami ya wakilta,ya yabawa hukumar ta NEMA akan samar da kayayyakin tallafin.
Gwamna Masari yace nan bada jimawa ba wadanda gobarar ta ritsa da su zasu dara, don a halin yanzu an kammala shirye-shiryen hannanta tallafinda gwamnati tayi alkawarin sama masu.
Daga nan sai ya hori yan kasuwar akan suyi kyakkyawan amfani da kayayyakinda aka sama masu.
Da suke magantawa babban jami’in hukumar ta NEMA na Shiyyar Kaduna tare da Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar ,Katsina Alhaji Babangida Muhammad Nasamu,sunce samar da kayan nada nufin rage wasu daga cikin wahalhalunda suke fuskanta.
A nashi jawabin, Shugaban Kungiyar Yan Kasuwa na Babbar Kasuwar ta Katsina Alhaji Abbas Labaran Albaba ya nuna godiya ga Hukumar ta NEMA akan tallafa masu.
Alhaji Abbas Albaba yayi roko ga Gwamnatin Jiha akan ta tabbatar da sama masu da tallafinda aka alkawarta kafin nan da Sallah Babba.