Hukumar dake bada tallafin gaggawa zata fara bada tallafin abinci ga Yan gudun hijira a garuruwan jahar Borno.
Wannan ya fito ne daga bakin Jagoran hukumar na yada labarai dake Jahar, Ibrahim AbdulKadir, ya bayyana hakan ga manema labaran Jaridar Vanguard a ranar Asabar.
Yace “Miliyoyin mutane ne wadanda iftila’in Bokoharam da Yan bindiga ya shafa suke samun tallafin daga hukumar.”
KARANTA:- TSARO: Jami’an Najeriya sun cafke wadanda ake zargin Yan bindiga ne guda 100
Shugaban hukumar ta Arewa maso gabas Lydia Madu Wagami, wadda take Jagorantar rarraba kayan tallafin, a wancan satin, ta jagoranci hakan a wasu sassa da suka hada da Jakana, Mainok da garin Beneishek, inda kimanin Mutane 35,508 suka amfana da tallafin.
“Bada tallafin kayan abincin wanda shugaban hukumar ta Kasa Alhaji Mustapha Habib Ahmad ya bada umarin hakan, wanda na daga cikin kudurin gwamnatin tarayya na tallafawa jahar Borno karkashin Jagorancin gwanma Alhaji Babagana Umara Zulum don rage radadin yunwa ha kunci kan Mutanen da yakin Bokoharam ya shafa.”
“Kowane gida zai sami tallafin kayan abinci wanda ya hada da buhun wake, buhun shinkafa, buhun masara da kayan sarrafawa kamar su gishiri, magi tumatiri, Mai da sauran su.” Kamar yadda Ibrahim ya bayyana.