Ministar Kudi, kasafi sa tsare-tsare Zainab Ahmed, ta sanya hasashen biyan kudin tallafin man fetur a kullum kan Naira biliyan 18.39.
Ta bayyana hakan ne yayin wani zaman bincike na kwamitin wucin gadi na majalisa wanda ke binciken tsarin tallafin man fetur tsakanin 2017 zuwa 2021.
“Jimillar adadin tallafi man a kowace rana shine biliyan 18.397 a kowace rana,” in ji ta. “Don haka idan kuna yin hasashen na tsawon shekara, zai zama tiriliyan 6.715. Idan kuna yin hasashen na rabin shekara, zai zama kashi 50 na hakan.”
A cewar Ministan, an kididdige hakan ne ta hanyar amfani da bayanan da Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) da hukumar kula da harkokin man fetur suka bayar.
Kotu Ta Ɗage Ranar Sauraron Ƙarar Da Ake Neman Haramta Wa Tinubu Takara A 2023
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ta ce bayanai sun nuna cewa lita miliyan 64.96 na man fetur ne da ake hasashen za a iya fitar da ita a kullum.
Ta kuma ce an biya Naira tiriliyan 1.774 ga ‘yan kasuwar mai masu zaman kansu a matsayin tallafi a cikin shekaru hudu.