A wani mataki na bin umurnin Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ma’aikatar kudi da na kananan hukumomi za su biya albashi ga ma’aikata, a yayin da wadansu ma’aikatan tuni suka fara samun na su albashinsu daga bankunansu tun ranar Talata.
Gwamnan ya bada wannan umurnin ne domin saukakawa ma’aikata a yayin da za a shiga watan Ramadan a daidai lokacin da ake yaki da cutar Korona.
Bisa wannan umurni dukannin masu ruwa da tsaki na gwamnatin jiha da kananan hukumomi sun bi wannan umurni wajen biyan wadannan albashi ga ma’aikata.