Gwamnatin Sakkwato a ranar Laraba ta ayyana dokar takaita zirga-zirgar Babura na Awa goma sha biyu a kananan hukumomi hudu da ‘yan bindiga suka fi kai hari a kwanakin nan.
Gwamna Aminu Tambuwal ne ya bayyana hakan a cikin wata sanawar da mashawarci na musamman kan harkokin kafafen watsa labarai na gwamnan, Malam Muhammad Bello ya fitar, jim kadan da kammala zaman da kwamitin tsaron jihar ya gudanar.
Tambuwal ya ce kananan hukumomin da wannan dokar ya shafa ya hada da; Isa, Sabon Birni, Rabah da Goronyo.