- Wata mata ta ce tana neman wanda zai iya aure da ita saboda ta ce ta kasance cikin kaɗaici bayan rabuwar ta da tsohon mijinta
- Ta ce tana da shekara 32 kuma a shirye ta ke ta ƙulla alaƙa da namiji mai shekaru 40 zuwa sama da haka.
- Ta aika da sakon sirri ga @oku_yungx, wanda ya wallafa a shafin Twitter, inda ya haifar da tsokaci
Wata mata ta koka inda ta ce tana neman wanda zai iya aure da ita saboda ta gaji da zaman kaɗaici.
Matar mai shekaru 32 ta aike da sakon da ba a bayyana sunanta ba ta hannun @oku_yungx a shafin Twitter, inda ta ce tana bukatar namiji a rayuwarta.
Ta ce bata da aure kuma ba ta da ɗa, wanda hakan ya sa take jin kaɗaici kuma tana buƙatar ɗa namiji cikin gaggawa.
KARANTA WANNAN LABARAIN: Wani Maigadi Ya Ɗirkawa Matar Ubangidansa Ciki Har Wata 5.
Matar ta ce tana son yin aure da maza masu shekaru 40 zuwa sama.
Ta ce mutumin da zai aure ta tana so ya kasance mai lafiya ne.
Kalamanta: “Barka da yamma. Ina da shekaru 32, na taɓa aure ba tare da ɗa ba, kaɗaici yana neman kashe ni, don Allah. Za a iya taimaka a watsawa al’umma ko za a samu masu maza masu shrkaru (40), waɗanda ke son dangantaka kuma wanda yake da lafiya. Ina da aiki kuma. Na gode.”
Sakon nata ya jawo martani da yawa daga masu amfani da shafin Twitter.
Masu amfani da Twitter sun mayar da martani yayin da wata mata ke neman wani mutum da zai aure ta
@roqzee ta ce: “Ana zaune lafiya ” a wannan tattalin arzikin Tinubu? Omo tana buƙatar daidaita wannan abin da take buƙata, har ma da maza sama ‘yan sama da 40. Sannan ba mu san ko wanda ya sake ya sake ta ne saboda tana dukan tsohuwarsa…abin da namiji zai yi mace zata yi sama da haka.”
@AimThaMachine_ yayi sharhi: “Wata mata ƴar shekara 32 da aka sake ta babu yara tana neman mutumin da bai kai 40 ba yana kuma da kuɗi a cikin wannan halin da Buhari ya barmu yanzu kuma Tinubu ya ƙara damalmala lamarin. Amma ba a bakina zaka ji ba”