A safiyar nan ne wasu motocin mai guda biyu suka yi haɗari wanda yayi sanadiyyar kama wuta, lamarin ya jawo cunkosu akan babban titin sakamakon shi ne titi tilo guda daya da ake amfani da shi wajen dauko kayan masarufi daga gabar bakin teku.
Hatsarin ya haddasa gagarumin cunkosu a hanyar wadda ta ita ake safarar daukacin kayayyakin masarufi daga gabar ruwa a Legas zuwa sassan Najeriya, kuma ita ce kadai mahadar Legas da sassan Najeriya.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto ‘yan kwana-kwana da sauran jami’an kare hadura na kokarin kashe wutar wadda ta yi sama da awa bakwai tana ci, ko da yake ba a samu asarar rai ba. Wani da ganewa idonsa ya shaidawa manema labarai cewa, ‘yan kwana-kwana sun yi kokari ta yadda wutar tankar ta tsaya ga manyan motocin biyu.
“Akwai karin wata motar tanka dauke da mai da ba ta kama da wuta ba, ita ake ta kokarin zuba wa ruwa domin gudun kada wuta ya tashi a kanta”, inji shi.