Wata tankar man dizal da ake tsammanin mallakin kamfanin Conoil PLC ne ta yi hatsari a kan hanyar Legas zuwa Ibadan, abin da ke cikinta ya zube. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Dimokuradiyya ta samu labarin cewa motar dakon mai ta kife ne a kan babbar hanyar, lamarin da ya yi sanadiyar cunkoson ababen hawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Ba Da Umarnin Kwace Gidaje Da Motocin Diezani Dake Abuja
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a kewayen gadar Kara, da ke wajen titin.
Mai magana da yawun hukumar FRSC a jihar Ogun, Florence Okpe, ta ce jami’an hukumar da na sauran takwarorinta sun yi tattaki zuwa wurin da lamarin ya faru.
Okpe ya kara da cewa jami’an hukumar kashe gobara sun yi bakin kokarin su don shawo kan lamarin da kuma dakile barkewar gobara.
“An shawarci masu ababen hawa da su yi taka-tsantsan lokacin da za su tunkari yankin da hatsarin ya faru sannan kuma su ba da hadin kai ga Jami’an da ke kula da lamarin.
“Ba a iya karkatar da ababen hawa ba saboda babu wata hanya kusa da wurin da hadarin ya faru. Don haka muna ba masu ababen hawa shawara da su kwantar da hankalinsu tare da bin wasu dokoki da ka’idoji masu sauki,” inji Okpe
A WANI LABARI KUMA: AU Ta Fara Zaman Sulhubta Gwamnatin Habasha Da Yan tawayen Tigray
A yau Litinin ne bangarorin dake yaki da juna a kasar Habasha za su yi wani zaman tattaunawa domin nemo hanyar magance yakin basasar da aka kwashe tsawon shekaru biyu ana gwabzawa.
Zaman Wanda Kungiyar kasashen nahiyar Afrirka ce ta shirya shi, zai samu halartar wakilan gwamnati da na ‘yan tawayen Tigray da za su hallara a Afrirka ta kudu.