Wata tankar mai, a ranar Juma’a, ta fashe a wani gidan mai da ke Ogidi — garin da ke makwabtaka da birnin kasuwanci na Onitsha, jihar Anambra.
Fashewar ta haifar da tashin gobara, wadda ta kone wani bangare na wurin da ake hada man. Wata majiya ta ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar Juma’a, a lokacin da tankar man da ke dauke da man da ke cikin gidan mai ta tayar da gobarar, lamarin da ya haifar da fashewa da gobara.
A cewar majiyoyin, “Akwai turnikewar hayaki a duk fadin yankin Ogidi. Tankar man fetur din tana kokarin sauke mai a gidan mai ne sai aka ga wata ‘yar tartsatsin wuta, amma kafin a kashe, tuni tankar ta fara ci gadan gadan, ta kone wani bangare na gidan man”.
Da yake tabbatar da gobarar, Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Anambra, Mista Martin Agbili, ya ce mutanensa sun kashe gobarar.
Ya ce, “da misalin karfe 09:53 na safiyar yau (Juma’a), mun samu rahoton tashin gobara a gidan man fetur da ke Mile 7th Mile, Ogidi. Mun baza motocin mu na kashe gobara da jami’an kashe gobara zuwa inda gobarar ta tashi. Hukumar kashe gobara ta jihar Anambra, Awka, Najeriya da hukumar kashe gobara ta tarayya sun kasance a can domin yakar gobarar. An dai shawo kan gobarar gaba daya kuma an kashe ta.
“Ba a yi asarar rayuka ba yayin da aka ceci gidan mai; gobarar ta shafi tankar. Musabbabin tashin gobarar ya faru ne sakamakon wata tartsatsin wuta da ta tashi a wurin da suke aikin sauke man” inji shi.
“Za mu ci gaba da gaya wa masu gidajen man fetur da su daina sauke mai a lokacin tsananin rana ko da rana. An fi son yin wannan aikin da dare ko kuma da safiya.”