Rahotanni na nuna cewar wata mota Tankar Mai ta yi sanadin mutuwar mutane biyu a a hedkwatar Katagum dake Azare.
Motar Man ta kama da wuta ne da misalin karfe 3 na dare a daidai lokacin da take sauke Mai a wani gidan Mai, ta kama da wuta kuma hakan yayi sanadin rasa rayukan mutane biyu.
Jaridar Punch ta rawaito cewa motar ta kama da wuta ne a daidai lokacin da take fitowa daga gidan Man, sai wata wayar wutar Lantarki ta fado akanta, wanda haka ya sa ta kama da wuta nan take.
Wata majiya ta bayyana cewa lamarin ya auku ne daidai shataletalen First Bank, dake kan hanyar zuwa babban asibitin Azare.
Da aka tuntubi kakakin hukumar ‘yan sandan jihar DSP Amhed Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin.
Wakili ya kara da cewa “Lamarin ya faru a ranar Juma’a da Misali karfe 3 na dare, amma direban motar ai mutu ba sai dai yaji rauni kuma yanzu haka yana karbar kulawa, wanda suka rasu kuma sun rasu sakamakon ceto da suka je bayan motar ta kama da wuta”.