Wata tankar man fetur dauke da akalla lita 40,000 ta kama da wuta a wata tashar motar Toyota da ke kan hanyar Oshodi-Apapa, babban birnin jihar Lagos.
Gani da ido sun shaidawa manema labarai cewa tankar man na cin tafiya ne ta birkice, inda ta fadi kasa, nan take kuma man fetur din da ta dauko ya fara kwarara.
KARANTA WANNAN: Atiku Abubakar, dan Nigeria na farko da aka fara yiwa riga-kafin COVID-19
Tuni dai aka ci gaba da killace wurin da hatsarin ya faru, yayin da jami’an hukumar kashe gobara, hukumar ba da agajin gaggawa LASEMA, hukumar kai daukin gaggawa ta kasa NEMA da sauran jami’an tsaro ke ci gaba da kai dauki.
Ya zuwa tattara wannan rahoto, babu tabbaci na jin rauni ko asarar rayuka. Ga bidiyon a cikin wannan labari da TVC News ta wallafa.
https://twitter.com/tvcnewsng/status/1347114035867758593