Shehu Sani, tsohon dan majalisar tarayya, ya ce ya kamata a bi dokoki da ka’idoji da aka shimfida wajen maye gurbin Alkalin Alkalan Najeriya CJN.
Sani ya bayyana haka ne biyo bayan rahotannin da ke cewa Mai shari’a Tanko Muhammad ya ajiye mukaminsa na alkalin alkalan Najeriya.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, Sani ya rubuta cewa: “Ya kamata wanda zai maye gurbin CJN ya bi ka’idojin da aka gindaya. Bai kamata a yi tsalle-tsalle ba domin a samu wanda zai dace da siyasa, bangaranci, addini ko kabilanci na masu mulki.”
KARANTA WANNAN LABARIN; https://dimokuradiyya.com.ng/yanzu-yanzu-cjn-tanko-ya-yi-murabus-sakamakon-cin-hanci-da-rashawa-da-tuhume-tuhume-daga-alkalan-kotun-koli-14/
A baya Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Muhammad ya yi murabus ne a daren Lahadin da ta gabata, saboda rashin lafiya da ya sa ya yanke hukuncin.
Har sai da ya yi murabus, rahotanni sun nuna cewa Mai Shari’a Muhammad na fama da matsanancin rashin lafiya.
Muhammad ya kasance mai shari’a a kotun kolin Najeriya tun shekarar 2005 kuma an nada shi a matsayin alkalin alkalan Najeriya a shekarar 2019.
Ya taba zama Alkalin Kotun daukaka kara ta Najeriya.
A Wani Labarin Kuma Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fice daga kasar a safiyar yau Litinin zuwa kasar Faransa bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Tunde Rahman na ofishin yada labarai na Tinubu ya fitar ranar Litinin, ya ce shugaban nasa ya tafi birnin Paris na kasar Faransa domin gudanar da wasu muhimman taruka.
Ya lura cewa ana sa ran dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zai dawo kasar nan ba da jimawa ba ba tare da bayyana takamaiman ranar ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito tun da farko kafin tafiyar tasa, Tinubu ya halarci taron baje kolin wani littafi mai suna, ‘Mr. Speaker’ and launch of legislative mentoring initiative in commemoration of the 60th birthday of the Speaker of House Representatives, Femi Gbajabiamila, a Abuja ranar Lahadi.