Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Cristiano Ronaldo Wanda Kuma ya lashe mai Ballon d’Or biyar, ya sake kafa sabon tarihi a kwallon kafa, inda ya ci wa kasar sa ta Portugal kwallaye a wasan da suka fafata da Ireland.
Jaridar Goal.com ta rahoto cewa, dan wasan gaba, ya shiga littafin tarihi ne ya yin da ya ci wa kasar Portugal kwallayensa na 110 da kuma na 111.
A jiya Laraba 1 ga watan Satumba n shekarar 2021, Ronaldo ya zarce Dan wasa Ali Daei a yawan kwallayen da aka ci wa kasa a tarihin kwallaon kafan Maza.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba mu da shirin tsige Gwamnan jihar Filato, inji Yan majalissar jihar
Ronaldo ya ceci Portugal a filin wasa na Estadio Algarve a minti na 89. Ana shirin tashi ne kuma dan kwallon ya sake jefa kwallo a ragar Ireland.
Kazalika wannan bashine karo na farko ba da Ronaldo ya saba ceton Kasar sa ta Portugal a kowani irin mataki na wasannna kwallon kafa.
Har’ila yau kwallayen da Ronaldo mai shekara 36 ya ci a jiya, na nuna cewa, ya zura kwallaye 111 ga kasar sa ta Portugal, Wanda hakan yasa ba a taba samun dan wasan da yake da yawan wadannan kwallaye ba, a tarihin kasar
Comments 2