Mista Kayode Ojo, jigo a jam’iyyar APC a jihar Ekiti ya roki amintattun jam’iyyar da su guji duk wani abu da zai iya kawo cikas ga babban taron jam’iyyar na ranar 2 ga watan Oktoba.
Ojo ya fadi hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan yada labaransa, Alhaji Deji Ayelabowo a ranar Laraba a Ado-Ekiti, inda ya bukaci dukkan membobin jam’iyyar da su kiyaye kyawawan dabi’u domin tabbatar da gudanar da taron cikin lumana.
A cewarsa, ya kamata babban taron jam’iyyar ya kasance cikin lumana da tsari sannan kuma ya zama darasi ga sauran jam’iyyun siyasa a jihar da ma kasa baki daya.
“Idanu duka suna kan wannna taron, saboda haka, ka da a bada damar kowanne irin rashin tsari; duka shugabannin jam’iyya da membobi dole ne su yi aiki cikin jituwa don tabbatar da cewa an gudanar da taron ba tare da wata matsala ba, ”in ji Ojo.
Ya yi kira da hadin kai tsakanin membobin APC domin ciyar da jam’iyyar gaba, ya kara da cewa APC ba za ta iya shiga zabuka tare da raba gida ba.
Ya yi alkawarin ci gaba da taka rawa a matsayinsa na masu ruwa da tsaki don karfafa jam’iyyar a jihar da Najeriya baki daya.
Ojo, duk da haka, ya bukaci membobin da su zabi kwararrun ‘yan takara a ofisoshi daban -daban don amfanin jam’iyyar don tabbatar da nasara a zabubbuka masu zuwa.
Ya yi kira ga membobin da su ci gaba da yin aiki don ci gaban da ci gaban jam’iyyar.
Ojo, daya daga cikin masu neman kujerar gwamnan jihar Ekiti a shekarar 2022, ya ba da tabbacin cewa, idan aka ba shi dama, zai tabbatar da cewa jam’iyyar ta samu nasarar lashe zabe a jihar.
Ya gargadi masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da su ba da dama ga dukkan masu son tsayawa takara, domin kada su kawo baraka a yayin zabe.
Gwamna Mai-Mala Buni ya jagoranci Kwamitin rikon kwarya na APC ya zayyana manyan tarurrukan jam’iyyar na jihohi a ranar 2 ga watan Oktoba a fadin kasar.