By Abbas Yakubu Yaura
Akalla ‘yan takara biyar ne suka mallaki fom din bayyana sha’awar su ta tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar APC gabanin gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa.
Farfesa Al-Mustapha Ussiju, daraktan tsare-tsare na jam’iyyar,da kwamitin tsare-tsare na musamman na jam’iyyar APC mai rikon kwarya ne ya sanar da sayar da fom din a wata sanarwa a ranar Talata.
Malam Saliu Mustapha da Abdullahi Adamu da tsohon gwamnan Nasarawa suna daga cikin ‘yan takara biyar da suka sami fom din neman takarar shugaban Jam’iyyar.
Tanko Al-Makura, tsohon gwamnan Nasarawa, da George Akume, ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, na cikin sauran masu bukatar.
Shi ma wani tsohon Gwamnan Zamfara, Mista Abdulaziz Yari, daga yankin Arewa maso Gabas, ya samu fom din duk da shugabancin jam’iyyar ya karkata zuwa yankin Arewa ta Tsakiya.
Daga yankin Arewa maso Gabas, ana rade-radin cewa tsohon gwamnan jihar Borno, Sen. Ali Modu Sheriff, na shirin karbar fom din neman takarar shugabancin jam’iyyar daga sakatariyar jam’iyyar ta kasa domin yin takara a babban taron kasa na ranar 26 ga watan Maris 2022.
Ana sa ran taron zai samu halartar wakilai kusan 4,000 daga sassa daban-daban na kasar inda za a zabi sabbin shugabannin jam’iyyar na kasa da za su tafiyar da harkokin jam’iyyar.
A ranar 16 ga watan Maris ne dai Jam’iyyar ta APC ta soke gudanar da taron ta na NEC wanda aka shirya gudanarwa a ranar 17 ga watan Maris bisa wasu dalilai.