A taron ranar Talata tsakanin shugabannin kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) da gwamnatin tarayya ya sake zuwa karshe ba tare da cimma matsaya ba.
Hakan na nufin yajin aikin da malaman jami’o’in gwamnatin ke yi na shirin ci gaba na tsawon watanni shida.
Malaman da suke yajin aikin sun gana da kwamatin Farfesa Nimi Briggs a ranar Talatar nan a hukumar jami’ar kasa da ke Abuja tare da fatan ganin an shawo kan matsalar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Wani jigo a ASUU da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa gidan talabijin na Channels cewa mambobin kwamitin sulhu na Briggs ba su zo da wani sabon tayi a kan teburin tattaunawar ba.
Kenya: Odinga Yayi Watsi Da Sakamakon Zabe, Zai Kalubalanci Nasarar Ruto A Kotu
A maimakon haka, majiyar ASUU ta ce, kwamitin ya roki malaman da su dakatar da yajin aikin da suke yi, tare da yin alkawarin cewa za a sanya damuwarsu a cikin kasafin kudin 2023.
Majiyar ta ce taron wanda aka fara shi da misalin karfe 12 na rana, ya shafe kusan sa’o’i uku ba tare da cimma matsaya ba.
Bukatun ASUU
ASUU ta shiga yajin aikin gargadi na makonni hudu a ranar 14 ga watan Fabrairu.
A ranar 14 ga watan Maris, kungiyar ta kara wa’adin aikin masana’antu da wasu watanni biyu domin baiwa gwamnati damar biyan dukkan bukatunta. An sanar da tsawaita makwanni 12 a ranar 9 ga Mayu.
Tun a ranar 9 ga watan Mayu kungiyar ta ci gaba da yajin aikin, inda ta sha alwashin ci gaba da yajin aikin har sai an biya bukatunta.
Malaman na neman ingantacciyar walwala, farfado da jami’o’in gwamnati da cin gashin kansu na ilimi da dai sauran bukatu.
Wani abu da ke damun malaman shi ne rashin biyan kudaden farfado da jami’o’in, wanda ya kai kimanin naira tiriliyan 1.1.
Sai dai gwamnatin tarayya ta ce ba ta da kudin da za ta biya irin wannan adadin, saboda karancin man fetur a zamanin gwamnatin Muhammadu Buhari.
An kulla yarjejeniyar a shekarar 2009.
Wani kuma shi ne batun Tsarin Biyan albashin ma’aikata da Tsarin Bayanai na Ma’aikata (IPPIS).
Malaman sun ba da shawarar tsarin biyan kuɗin albashi na daban, ta hanyar tabbatar da adalci da kuma daidaito shi ne mafita (UTAS).