‘Yan Nijeriya ma’abota amfani da shafin sada zumunta na Twitter sun yi wa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai rubdugu.
Mabiya Twitter din sun zargi gwamnan da tauye haƙƙi, inda wannan ya zama kusan shi ne abin da ake tafka muhawara a kai kan gwamnan jihar Kaduna Nasir Elrufa’i tun safiyar wannan Juma’ar a shafukan sada zumuntan Nijeriya.
Wannan kuwa ya biyo bayan gayyatar da ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa, NBA ta yi wa gwamnan domin halartar taronta na ƙasa da ta shirya gudanarwa, wanda ya gamu da suka.
Sai dai abu kamar wasa wannan batu ya zama babba domin tun a ranar Alhamis ƙungiyar Lauyoyin ta sanar da janye gayyatar da ta yi wa gwamnan sakamakon adawar da wasu lauyoyi suka rinka nuna wa.
Wannan batu a yanzu ya kasance abin da ke jan hankali inda wasu ke suka wasu kuma ke yaba matakin ƙungiyar lauyoyin.