An kai wa Tashar Nukiliyar ce dake kusa da birnin Tehran hari da makami mai linzami a ranar Lahadi, inda Iran harin ta’addanci ne duk da kasancewar babu wanda ya mutu ko ya jikkata kana babu wata gurbataccen sinadari da ya fantsama.
Wannan hari na zuwa ne kwanaki bayan da aka sake komawa tattaunawar Vienna kan makomar Makamashin Nukiliyar Iran din tun a shekarar 2015 tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi watsi da tattaunawar.
To sai dai Magajin Trump Joe Biden ya nuna aniyar shi ta ci gaba da sake tattaunawar kan yarjejeniyar tsagaita makamashin nukiliyar da manyan kasashen duniya masu karfin fada a ji, muddin Iran ɗin na son kaucewa kakaba mata takunkumin tattalin arziki.
A baya dai gwamnatin Iran ta nuna yatsa wa Isra’ila Kan wasu hare haren da aka kai mata ciki har da na kisan watan Nuwambar Bara da aka yi wa babban jami’in ta mai kula da makamin nukiliyar.