By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mafarautan hudu ne suka mutu, yayin da wasu bakwai suka samu raunuka daban-daban, lokacin da wani abin fashewa ya tashi dasu wanda ake kyautata zaton masu tada kayar baya ne suka binne a kan babbar hanyar Borno a ranar Asabar din da ta gabata, kamar yadda wata majiyar mafarautan yankin ta bayyana.
DUBA WANNAN LABARIN: Jam’iyyar APC Ta Yi Allah-Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ondo
An tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na safe a tsakanin Damboa zuwa Sabon-Gari kan babbar hanyar Damboa/Biu a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.
An tattaro cewa motar da suke aiki ta lalace ba za a iya gyara ta ba saboda a halin yanzu mafarauta bakwai na cikin mawuyacin hali.
Wani mafarauci mai suna Bura Mohammed ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa sun je sintiri ne a lokacin da suka taka nakiyar.
Ya ce tuni aka yi jana’izar wadanda abin ya shafa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Sannan yace sauran mafarautan da suka samu raunuka daban daban suna samun kulawar likitoci a babban asibitin Biu.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, rundunar sojin ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba.
Comments 1