A sabbin jihohin arewa da aka samu masu dauke da cutar Korona, jihar Gombe na ciki, inda NCDC wato Cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, suka tabbatar da samun mutane 5 ringis a karon farko masu dauke da Korona daga Gombe.
Sun wallafa hakan ne a shafinsu na Twitter a daren ranar Litinin.
Hakazalika ma a Sokoto an samu mutum na farko mai dauke da cutar.