Dayake magana a wajen taron a matsayin sa na Shugaban kwamitin inshora bankuna, da Sauran harkokin kudi bayan ya rubuta a shafinsa na Facebook, game da yadda taron ya gudana, Sanata Uba Sani Mai wakilitar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattijan Nigeria. Ya na mai cewa, daga ranar Alhamis 15 ga watan Yuli zuwa Ranar Asabar, 17 ga watan Yulin Shekarar 2021, Kwamitin Majalisar Dattawa a kan Bankuna, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudin da na ke shugabanta, mun yi Zama na daban-daban da Hukumar Kula da Kadarori ta Nijeriya wato (AMCON), da kuma hukumar zuba kudi na Inshora ta Nigeria (NDIC), a Bafra International Hotel dake Kaduna.
Ma Halarta taron da kuma yadda aka gudanar da taron bisa tsarin tafiya na musamman a fannin Cigaban Tattalin Arziki da kuma dorewar shi, bisa aikin NDIC,” da “Maido da kadarori a matsayin wani hubbasa, da gudummawa ga bunkasa tattalin arziki da ci gabansa, da Kalubale da maƙasudin maido da Kadarorin Nigeria, duk a cikin kwarewar AMCON. ”
Sanatan ya kara da cewa, “A cikin jawabina a wuraren taron daya gabata, na nuna mahimmanci ga dabarun AMCON da NDIC na farfadowar tattalin arzikin Nigeria, da kokarin dai-dai-ta wa musamman wajen tabbatar da dai-dai-tuwar harkokin kuɗi, “NDIC cibiya ce mai mahimmanci wacce dole ne majalisar kasa, ta yi duk abin da zata iya, domin tabbatar wa, da kuma yin aiki yadda ya kamata. An kafa NDIC ne da nufin ba da gudumma wa ga tsarin kuɗi, domin Samun damar ɗorewarsa da kare ƙananan masu ajiyar kuɗaɗe ta hanyar samar da ingantacciyar hanyar warwarewa, da biyan diyya a cikin yanayin kunci na gazawar cibiyoyin na inshorar su. ” Inji sanatan
Game da Hukumar Kula da Kadarori ta Nigeria (AMCON), na bayyana cewa “Tun lokacin da aka kafa AMCON a shekarar 2010, Majalisar dokoki ta kasa ta himmatu, don karfafa tsarinta na doka da na hukumomi don ba ta damar bayar da gudumma wa mai kyau ga namu kokarin na dawo da tattalin arziki da kokarin dai-dai-ta wa. Majalisar Dokoki ta Kasa ta yiwa dokar kwaskwarima a shekarar 2015 da 2019. Dangane da tasirin cutar Covid-19 kan manufofi da aiwatar da AMCON. Har’ila yau Majalisar Dattawa ta yi wa dokar kwaskwarima a cikin wannan Shekara ta 2021, ta hanyar fadada yadda yake aiki da kudin Resolution Cost Fund, da kuma bawa AMCON ikon shiga kotu, Musamman da BOFIA ta kafa, a shekarar 2020 don magance al’amuran da suka shafi kudi. ”
A cikin jawabinsa a karshen taron Manajan Daraktan NDIC, Mista Bello Hassan ya ce, yana farin cikin sanar da mahalarta taron, tare da hadin gwiwar sauran manyan masu ruwa da tsaki cewa, sun kasance masu himma wajen da kula da kasadar da ke tattare da Kuma rashin tsaro. Inda ya Kara da cewa, NDIC ta dauki mahimman matakai wajen tabbatar da tsaron bankuna a Nigeria, da kuma kare masu ajiya a cikin lamuranta. Misali, hukumar NDIC a shekarar 2020 ta kafa ‘FinTech, da Innovation Unit’ don magance kalubalen barazanar yanar gizo ta Cyber), da sauran kalubalen FinTech na wasu abubuwan kirkire-kirkire, da kamfanin ya yi amfani da wannan dandalin don fara daukar matakan kulawa kan bankunan zamani, (Digital Bank), inganta matakan kariyar musamman ma game da masu ajiya a sashin asusun zamani, ta hanyar inganta hadin gwiwa da sauran masu sarrafa gidan na yanar gizo a duk matakin tsaro.
KARANTA WANNAN LABARIN: “Sakamakon Gwajin Lafiyar Muhuyi na bogi ne”~ inji wani Masani.
Sanata uba sani ya ce, a nasa gudummawar, Mista Ahmed Kuru, Manajan Daraktan AMCON ya bayyana cewa, babbar cibiyar ta kwato kadarori ta, samu cigaba matuka a kokarin ta na dawo da bashi AMCON ya zuwa yanzu ta dawo da kimanin Naira tiriliyan N1.4. Ya ce kuma ya na da kwarin gwiwa cewa, idan AMCON ta ci gaba da kokarin dawo da bashin a yanzu da kuma kawar da kadarorin, a cikin shekaru 15 za ta sauke nauyin da ke kanta ga Babban Bankin Najeriya (CBN).
“Tattaunawar a wuraren taron biyun sun kasance masu ban Sha’awa, a bayyane tare da hangen nesa. Anyi nazari a tare na kwarewa kan kalubalen, ya kuma kara fahimtar da membobin kwamitin dabarun, da matsayin AMCON da NDIC a cikin tattalin arziki, musamman a fannin tsarin kudi. NDIC da AMCON sun raba tunaninsu ga membobin taron a kan hanyoyin da za’a karfafa su ta hanyar doka da kuma tsari don tabbatar da kyakkyawan aiki. Kwamitin ya ba AMCON da NDIC tabbacin aniyarsu ta zurfafa kawance da manyan cibiyoyin biyu. Mahalarta taron sun tafi da wasu matakai wadanda za a iya amfani da su, wadanda idan membobin Kwamiti, NDIC da AMCON za su bi su, kuma za su aiwatar da su, za su sake kafa manyan cibiyoyin biyu tare da taimaka wa wajen gaggauta farfadowar tattalin arzikinmu” inji Sanata Uba Sani
Comments 1