Kwamitin hadin gwiwa na kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya da kungiyoyin da ba Malamai ba, ya ce babu wata nasara da aka samu a zaman da kwamitin sulhu yayi da gwamnatin tarayya.
Da yake magana a wata tattaunawa da manema labarai a ranar Talata.
Mataimakin shugaban kungiyar SSANU na kasa, Dr. Abdussobur Salaam, ya ce kwamitin ya gana da SSANU sau daya kacal tun bayan kaddamar da kungiyar a ranar 7 ga Maris, 2022.
Kwamitin, wanda Uban Jami’ar tarayya ta Alex Ekwueme Ndufu-Alike, Emeritus Farfesa Nimi Briggs ya jagoranta, an baiwa kwamitin wa’adin watanni uku ya kammala tattaunawa da kungiyoyin jami’o’in hudu tare da aika rahoton ga gwamnatin tarayya.
Wa’adin kwamitin ya kare ranar Litinin.
Ana kyautata zaton kwamitin zai mika rahotonsa ga gwamnatin tarayya a cikin wannan mako ko kuma ya samu karin wa’adi.
Sai dai Salaam ya bayyana cewa huldar kwamitin Briggs da SSANU bai yi kadan ba kuma ba a bi ka’ida ba.
Ya ce, “A cikin wa’adin watanni uku, SSANU ta yi ganawa daya ne kawai da tawagar sake tattaunawa da Briggs.
An gudanar da taron ne a ranar Juma’a 8 ga Afrilu, 2022, kasancewar 7 ga watan Yuni ya yi daidai da watanni biyu da suka gabata wato dai lokacin da kungiyar ta fara Yakin aiki.
Kungiyar SSANU ta fara yajin aikin gargadi na makonni biyu wanda ya fara a ranar 27 ga Maris, 2021, yayin da karin wasu makonni biyu ya fara a ranar Lahadi, 10 ga Afrilu, 2022.
Bukatun kungiyar sun hada da batun tsarin hada-hadar biyan albashi da bayanan ma’aikata, da rashin biyan alawus-alawus, da kuma jinkirin sake tattaunawa kan yarjejeniyar gwamnatin tarayya, NASU, SSANU, da rashin biyan mafi karancin albashin ma’aikata.
Sauran sun hada da sakaci da rashin samun kudaden shiga da jami’o’in gwamnati ke yi, da rashin biyan ‘yan kungiyar da suka bar aiki kudaden ritaya, da kuma kwace shugabancin sassan da ba na koyarwa ba, wanda ya saba wa sharuddan aiki da tsarin kafa da dai sauransu.