Tawagar gwamnatin jihar Kano a karkashin mataimakin gwamnan jihar, Dr Nasiru Yusuf Gawuna ta kai wa tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso ziyarar ta’aziyyah bisa rasuwar mahaifinsa.
Tawagar ta hada da Kwamishinoni, mashawarta, da kuma shubannin hukumomi da ma’aikatu na jihar.
A yayin da yake mika sakon ta’aziyyar a madadin gwamnatin jihar, Gawuna ya ce; suna mika sakon ta’aziyyarsu bisa rasuwar Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, Makaman Karaye. “rasuwarsa babban rashi ne ba kawai ga kai ba ga mutanen jihar Kano baki daya”. Ya tabbatar.
A karshe ya yi addu’ar Allah yasa aljanna Firdausi ce makomarsa, sannan Allah ya bai wa iyalai hakurin jure rashinsa.
Da yake maida bayani, Rabiu Musa Kwankwaso ya godewa mataimakin gwamnan bisa wannan ziyarar.