Rahotanni daga birnin Tehran sun tabbatar da cewar, wata tawaga mai karfi a bangaren siyasa ta kungiyar Taliban ta isa birnin Tehran na Iran,domin tattaunawa da hukumomin Iran kan lamarin samar da zaman lafiya a kasar Afghanistan.
Tawagar wacce babban jami’in Taliban a bangaren Siyasa da difulomasiyya Mullah Abdul Ghani Baradai ke jagoranta,ta isa birnin Tehran a ranar Talata 26/1/2021 domin tattaunawa game da yadda za’a samar da zaman lafiya mai dorewa a Afghanistan din.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatibzedeh ne ya bayyana hakan a wani taron da yayi da manema labarai a birnin Tehran din.
Ya bayyana cewar, tawagar yan Taliban din zasu gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif, sannan zasu yi wasu taruka na sirri a tsakaninsu su yan Afghanistan din da kuma wasu manyan jami’an gwamnatin Iran domin samo bakin zaren warware matsalolin tsaro a kasar Afghanistan.
Khatibzadeh ya bayyana cewar, Iran tana goyon bayan tattaunawa tsakanin yan Afghanistan din yasu-yasu kuma Tehran zata amince da duk matsayar da zasu cimma, kuma zata taimaka musu wajen ganin an samu nasara kan wannan batun.
An fara wannan tattaunawar ce tun lokacin da Amurka ta bayyana cewar zata kwashe dakarunta kimanin 12,000 daga Afghanistan din,bayan ta sha matsin lamba daga gwamnati da kuma dakarun Taliban din.