Shahararriya ‘yar wasan gasar tennis ɗin nan kuma ‘yar asalin ƙasar Romenia wadda a halin yanzu itace ta biyu a ɓangaren mata a jerin jaddawali da aka fitar a watan Satumba na shekarar 2020 wato Simona Halep ta yi wani furuci bayan ta lashe gasar wasan tennis ta Italian Open da aka kammala a wannan makon.
Ta zamo zakara ne bayan da tun a zagayen farko ta sami nasara a kan abokiyar karawarta daci 6 da nema, wannan shine karo na uku a kusan jere tana buga wasan ƙarshe na gasar Italian Open inda a wasanni guda biyu na baya duk ta yi rashin nasara wato a shekarar 2017 da kuma shekarar 2018, amma kuma yanzu gashi a shekarar nan ta 2020 ta lashe gasar kai tsaye inda tayi wasan bajinta a wasan na ƙarshe data fafata inda wasan ya ƙayatar da masu kallo sosai.
‘Yar wasan dai a halin yanzu tana da shekaru 28 a duniya inda take amfani da hannun dama wajen yin wasan tennis kokuma wani lokacin tayi amfani da hannunta na hagu, sai dai Simona tasha lashe ƙananan gasussuka na tennis sosai da sosai wanda ƙoƙarin da ta keyi nema yasa take a matsayi na biyu na gasar ta tennis a duniya a halin yanzu.
Gasar Italian Open bata daga cikin gasa mai daraja ta farko a duniyar tennis, kwanannan aka kammala gasar U.S Open wadda tana daga cikin gasa mai daraja ta farko inda Simona Halep bata halacci gasar ba badan komai ba sai don tsoron cutar nan data dabaibaye duniya ta Coronavirus inda matashiyar ‘yar wasa Naomi Osaka ta zamo zakara kuma take ci gaba da kafa tarihi a duniyar ta tennis.
Daga cikin gasa mai dara ta farko dai Simona Halep guda biyu ta lashe, inda ta lashe French Open a shekarar 2018 sannan kuma ta lashe Wembledon Open a shekarar 2019, sai dai tunda take bata taɓa lashe U.S Open ba sannan bata lashe Australian Open ba, amma kuma a nan gaba za a fafata gasar French Open wadda ake yiwa laƙabi da Roland Garos inda Simona ta bayyana cewar yanzu burinta shine ta sake lashe gasar ta French Open.
“Na sake lashe wata gasar wadda na tabbatar itace karo na uku, bazan matsantawa kaina ba, nasan na buga wasa mai kyau musamman wasan da nayi akan yunɓu kuma zanci gaba da jajircewa sosai da sosai. Ina godiya ga masoya na domin wannan nasara ta sakani murmushi sosai da sosai, kuma inason naci gaba da kasancewa a cikin farin ciki ako da yaushe”
Simona dai bayan kammala wannan gasa ta Italian Open da aka yita a birnin Rome na ƙasar Italia hakan ya muna cewar lallai ta shirya tsaf a gasar French Open daza ayi a nan gaba wanda tabbas itama gasar tana daga cikin gasa mai daraja da farko wadda duk wanda ya lashe ta to ya kafa tarihi a duniyar tennis.
A cikin wannan shekarar ta 2020 wannan itace gasa ta uku da ‘yar wasan ta lashe, idan za a iya tunawa ta lashe gasa a ƙasar Dubai a watan Feburairu sannan kuma ta buga wasanni 14 a jere ba tare da ta yi rashin nasara ba inda zata ɗora daga inda ta tsaya a gasar da za ayi a shekarar nan da ake ciki a can ƙasar Faransa mai taken Roland Garos.