Matashiyar ‘yar wasa Swiatek ta zamo zakara a gasa mai daraja ta farko a duniyar Tennis da ake yiwa laƙabi da Roland Garros, ta zamo zakara ne a ɓangaren mata bayan data doke abokiyar karawarta daci 6 – 4 da kuma 6 – 1 awasan ƙarshe da suka fafata.
Wasan ya baiwa mutane mamaki sosai ganin yadda wannan matashiyar ‘yar wasa ta ragargaza abokiyar karawar tata kuma ta wujijjigata tayimata dakan sakwarar Lagos a wasan ƙarshen na Tennis mai taken French Open wanda kuma ake kira da Roland Garros da aka gudanar dashi a can ƙasar Faransa.
Ita dai wannan matashiyar ‘yar wasa wadda ta zamo zakara duka-duka shekarunta 19 a duniya sannan kuma a jerin jaddawalin matsayin ‘yan wasa a duniya tana koma baya inda take a matsayi na 54 a duntake yayin da ita kanta wadda aka doke tana matsayi na 6 a duniya. Sai dai bisa wannan nasara da ‘yar wasan ta samu ana ganin zata iya dawowa sama-sama domin sake matsowa a jaddawalin na ‘yan wasan Tennis.
Wannan shine karo na farko da ‘yar wasan ta lashe gasa mai daraja ta farko tun bayan lokacin data fara fafata wasan gasar ta tennis a duniya wato gasa mai taken Grand Slam.
Daga ƙarshe bayan ta lashe gasar ta bayyana farin cikinta inda taji kamar a mafarki na wannan nasara data samu duba da yadda farin ciki ya mamayeta sosai da sosai a wasan ƙarshen data fafata kuma ta zamo zakara duba da cewar sunanta ya shiga kundin tarihin ‘yan wasan da suka lashe gasar French Open.