Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta dakatar da wasu manyan jami’an ‘yan sanda biyu saboda “dabi’a mara kyau” da kuma karya manufofin rundunar a kafafen sada zumunta.
Gidan talabijin na channels ya rawaito cewa, Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Juma’ar nan cewa an dakatar da jami’an, dukkansu mata ne ba tare da bata lokaci ba, “saboda saba dokar ‘yan sanda ta 2020, da kuma ka’idojin ‘yan sandan Najeriya na daukar ma’aikata da girmamawa da da’a na Supernumerary Police (SPY) 2013 da babban Sufeto Janar na ‘yan sanda, kamar yadda aka dauka a cikin wani faifan bidiyo da daya daga cikin jami’an ya saka”.
Karanta kuma: IGP Ya Dakatar Da ‘Yan Sanda Tara Saboda Jagorantar Yajin Aikin Da Aka Shirya Yi
Adejobi ya bayyana sunayen ‘yan sandan da Obaze Blessing mai lamba 5709 SPY, da Obaze Emmanuella Uju mai lamba 5708.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Bidiyon jami’an biyu sun yi yawo akan TikTok kwanan nan kuma kakakin ya lura cewa ɗayan bidiyon su ya yi hoto a ranar 3 ga watan Agusta, 2022.
Ya ce, a cikin faifan bidiyon, jami’an “sun yi ado da kan su cikin kakin jami’an ‘yan sanda na al’ada sabanin ka’idar da ke kula da aikin leken asiri. Hakazalika daya daga cikinsu ya kawata mukamin Sufeto na ‘yan sanda wanda ya saba wa dokokin.
“Fiye da duka, sun bayyana kansu a cikin faifan bidiyo da wasu faifan bidiyo a matsayin marasa da’a da kuma rashin bin doka, wanda ya saba wa ka’idar ‘yan sanda ta shafukan sada zumunta, tare da ayyukan almubazzaranci, da rashin da’a, wanda ya sha Allah-wadai daga jama’a .”
A wani labarin kuma: Hukumar ‘Yan Sanda Ta Dakatar Da Jami’anta 2 Da Suka Yi Aiki A Karkashin DCP Abba Kyari
Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta dakatar da wasu ‘yan sanda biyu bisa zarginsu da hannu a safarar miyagunb kwayoyi.
Jami’an,sun hada da Sunday Ubua, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (ACP) da James Bawa, mataimakin Sufeton ‘yan sanda (ASP) an mika su ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA domin gudanar da bincike.