Inetimi Timaya Odon, wanda aka fi sani da sunaTimaya, ya ce baya son kara fadawa cikin yanayin soyayya.
Fitaccen jarumin ya yi wannan addu’a a shafinsa na Twitter.
“Kada ALLAH Ya bar ni in fada cikin Soyayya,” ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Mawaƙin Najeriya kuma marubucin waƙa, wanda ya fito daga garin Odi na jihar Bayelsa, shi ne ya kafa kamfanin DM Records Limited.
Timaya, wanda har yanzu bai yi aure ba, ya taba bayyana kansa a matsayin “Baby-Dady ” a duniya.
Duk da cewa yana son ‘ya’yansa, Amma duk da haka, ba ya so ya sake yin soyayya.
Sakon nasa ya zo ne makonni kadan bayan da jaruma Caroline Danjuma da jaririyar mawakiyar suka yi bikin suna a shafukan sada zumunta.