Daraktan yada labarai da dabarun yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Dele Alake ya kare tushen arzikin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, inda ya ce ya san Tinubu yana da arziki tun kafin ya shiga harkokin siyasa.
Alake, wanda ya yi wannan ikirari a wata hira da gidan talabijin na Channels Sunday Politics, ya lura cewa Tinubu ya yi kasuwancinsa da ciniki kuma yana da hannun jari tsawon shekaru don gina dukiyarsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana Fargabar An Kashe ‘Yan sanda, Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kaiwa Ifeanyi Ubah Hari
Ya alakanta tushen arzikin Tinubu da saka hannun jari a kamfanonin blue chip.
Alake ya ce, “Ya samu kudin sa sosai kafin ya shiga ofis. Ina ganin abin da ke da muhimmanci ga ’yan Najeriya, a gaskiya, shi ne su sani cewa wannan mutumin ba talaka ba ne kafin ya hau mulki, kamar yadda wasu ke tunani.”
Sai dai Alake bai bayyana ko Tinubu ya mallaki ko kuma yana da hannun jari a wani kamfani a Najeriya ba.
Ya ce, “Mene ne kasuwanci na game da kamfanin da ya mallaka a Najeriya? Idan gobe ka zama kamar Bola Ahmed Tinubu me zai sa na damu da kamfanonin da ka mallaka matukar ba a tabbatar da cewa ka kwashi kudin jiharka ba ko kamfanin da kake yi wa aiki?
“Ba a tabbatar da hakan ba kuma ba a gurfanar da ku a wata kotun shari’a ba. Me yasa yanzu zan dame kaina?”
“Wannan lamari ne mai ban mamaki kuma, kamar yadda na fada a koyaushe, damuwa da son zuciya na masu tsananin kishi da fama da OCH, kiyayya mai tilastawa, ga Asiwaju,” in ji.
A wani labarin kuma, Kotu Ta Yi Sammacin Gwamnatin Tarayya Da ASUU Kan Yajin Aiki
Kotun masana’antu ta kasa, NIC, ta yi sammacin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, da su gurfana a gabanta a ranar Litinin a Abuja, kan yajin aikin da kungiyar ta shiga tsahon watanni takwas da suka gabata.
Wannan sammacin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ta yanke shawarar mika takaddamar da ta ki ci ta ki cinyewa a tsakaninta da ASUU ga kotun NIC.