Daga: Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar kare hakkin Musulmi MURIC ta ce limaman cocin da suka halarci taron kaddamar da abokin takarar Bola Tinubu, Kashim Shettima ba na bogi ba ne.
Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya fitar da wata sanarwa a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan kalaman kungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN.
KARANTA WANNAN LABARIN; https://dimokuradiyya.com.ng/da-%c9%97uminsa-kotu-ta-aike-da-tsohon-akanta-janar-ahmed-idris-mutane-2-gidan-yari/
Akintola ya ce duk da irin yadda aka yi ta yada tikitin Musulmi da Musulmi, “Bishop da Fastoci da yawa” sun halarci zuwa wurin taron.
MURIC ta zargi shugabancin Kirista da nisantar gaskiya da rayuwa cikin musun kai.
“Binciken yanzu ya bayyana a fili cewa shugabannin CAN sun nisanta kansu daga gaskiyar,” in ji ta.
“Yaya kasa mai addini zai sauko? Menene CAN zata iya samu ta wajen yaudarar mabiyanta?
MURIC ta kuma zayyana wasu daga cikin wadanda ta kula da su limaman gaskiya ne da suka halarci wurin taron na jam’iyyar APC.
Akintola ya ce Bishop Kamoru “da gaske malami ne daga cocin Peace Chapel, dake Mararaba” a jihar Nasarawa.
“Hoto ya bayyana inda aka gan shi yana gudanar da bikin aure a cocin. Wasu ’yan uwa sun zo sun ce sun san shi da kansa.
“Reverend Father Hyacinth Alia, na cocin Gboko Catholic Diocese, jihar Benue, shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC.
MURIC ta lura cewa CAN “ba za a amince da ita ba” don CAN ta musanta “amma bishops da fastoci masu ilimi ne”.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan ya nuna cewa wata kungiya a cikin shugabancin kungiyar ta CAN ta kaddamar da mulkin kama karya a kan Kiristendam a Najeriya”.
Ugo Ugokwe, dan jam’iyyar APC kuma daya daga cikin malaman addinin, ya mayar da martani ga masu suka a wani sako da ya wallafa a Facebook ranar Laraba.