Jam’iyyar APC mai mulki ta kara Kwarzanta dan takararta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, inda ta ce shi dan siyasa ne na kasa wanda ya fahimci mafarki da burin matasan Najeriya.
Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na kasa, Yakubu Ajaka ne ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar tare da wasu daga cikin matasan Najeriya mazauna kasashen waje, a daren Asabar a birnin Landan.
Wannan ikirari na Ajaka ya dan bambanta da ra’ayin da masana siyasa ke yi na cewa talakawan Najeriya sun fi son dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi, wanda suka ce yana da akidar da ta dace da matasa.
DUBA WANNAN LABARIN: Amurka da NATO babbar barazana ne ga kasa – Rasha
Toh sai dai mataimakin kakakin jam’iyyar APC ya yi amanna da akasin haka, yana mai cewa hayaniyar Obi ta ta’allaka ne a shafukan sada zumunta.
Ya ce, “Ina da yakinin babu shakka cewa Tinubu ne kadai ya fi fahimtar matasa, zai iya baiwa matasanmu da kuma matasa a kasashen waje damar shiga da kuma bayar da gudumawarsu wajen sake samar da wata sabuwar Najeriya.
“Yana da damar hada abubuwan da suka shafi majalisa da zartarwa don samun hadin kai da ci gaban Najeriya wanda sauran ‘yan takara ba su da shi.
A matsayinsa na gwamna a yankin Kudu maso yammacin Najeriya, Tinubu bai yi daidai da kowa ba, ya kuma dauki ayyukan matasan Najeriya daga wasu jihohi domin ya yi aiki a majalisarsa.”
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin nan Ajaka ya karfafa gwiwar matasa musamman wadanda ke kasashen waje, da su yi kokarin sauya labaran cin hanci da rashawa da kuma barin su a baya da ake yi.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa hakan na zuwa ne a daidai lokacin da zaben 2023 ya rage kasa da watanni bakwai, idan kuma anan ne za a banbance tsakanin aya da kuma tsakuwa.