Tinubu-Shettima: CAN na fama da rikicin Ƙwaƙwalwa — MURIC
Ƙungiyar Kare Hakkin Musulmi MURIC ta caccaki Kiristoci ta Najeriya CAN, akan matsayar ta a zaɓin da Bola Tinubu yayi na tsohon Gwamnan Jahar Borno Bola Tinubu a matsayin wanda zaiyi masa Mataimaki a Babban Zaɓen Shekarar 2023.
Ƙungiyar Kare Hakkin Musulmi ta ƙalubalanci Ƙungiyar Kiristoci da yin munanan Kalamai akan zaɓin Tinubu na Tsohon Gwamnan Jahar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin Takara.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Ina Fatan Yarabawa zasu Zaɓi Tinubu — Sanwo-Olu
Sakon MURIC na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Ƙungiyar Farfesa Ishaq Akintola ya sanyawa hannu a ranar Talata.
“Tinubu yana shan kwankwatsa daga CAN na zaɓar Musulmi Sanata Kashim Shettima akan zaɓar shi, kuma Rabaran John Hayab shine Wanda ya yankewa Ƙungiyar CAN cibiya,” Cewar MURIC.