Tinubu ya ƙaryata neman Biliyan 50 duk wata daga Tsohon Gwamnan Legas — Ambode
Dan Takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu ya musanta rahotannin da ke cewa ya bukaci Tsohon Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode ya biya naira biliyan 50 duk wata a lokacin gwamnatinsa.
DAILY POST ta rahoto cewa Ambode wanda ya zama gwamnan jihar a shekarar 2015, ya shafe shekaru hudu ne kacal a kan karagar mulki yayin da yunkurinsa na neman wa’adi na biyu ya ci tura bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a 2018..
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan bindiga sun kai hari kan jami’an Immigration, sun kashe daya, sun jikkata biyu a Jigawa
A kwanakin baya ne wani rahoto ya bayyana a yanar gizo yana zargin cewa wani bangare na rashin samun tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a 2018 shi ne kin mika wa Asiwaju kudaden.
Da yake karyata rahoton a ranar Talata, wata sanarwa da Daraktan watsa labarai da sadarwa na kungiyar yakin neman zaben Tinubu (TCO), Bayo Onanuga ya ce Tinubu ba zai iya yin irin wannan bukata ba.
“Tsarin maganar yana cikin shaidun da ke nuna cewa Legas ba ta fara cika Naira biliyan 50 ba sai bayan da Ambode ya bar mulki.
Sanarwar ta kara da cewa “Tinubu ba zai iya neman biyan biliyan daya a kowane wata daga hannun Ambode ba a lokacin da gwamnatin jihar ba ta biya hakan ba a cikin wata guda a tsawon mulkin Ambode”.
Sanarwar ta bayyana cewa, an bayyana shafin da wasu labaran karya suka fito a matsayin Duniyar Labarai tare da URL a matsayin labaran duniya.
A cewar Onanuga, “Binciken da aka yi a shafin ya nuna karara cewa dandalin labarai ne na Biafra”.