By Abbas Yakubu Yaura
Wani jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya baiwa gwamnatin jihar Neja gudunmawar Naira miliyan 50, domin ta taimaka wajen magance matsalolin tsaro a jihar.
Hakan ya faru ne a wata ziyarar da ya kai gidan gwamnati da ke Minna inda Gwamna Abubakar Sani Bello ya tarbe shi a ranar Alhamis.
Tinubu Support Group ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, yana mai cewa, “Asiwaju a Minna, ya baiwa gwamnatin jihar tallafin naira miliyan 50 domin tallafawa matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki bayan da jigo a jam’iyyar APC ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 50 ga iyalan wadanda aka kashe a baya-bayan nan a kananan hukumomi biyu na jihar Zamfara.