Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya dawo Najeriya.
A ranar Lahadi ne Tinubu ya dawo Najeriya daga kasar Birtaniya da misalin karfe 8 na dare.
Jirgin da ke dauke da jagoran jam’iyyar APC na kasa ya isa filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas inda wasu shugabannin tawagar yakin neman zaben sa suka tarbe shi.
Makonni kadan da suka gabata Tinubu ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.
Jim kadan bayan da ya yi tsokaci kan tsayawa takarar kujera ta daya, tsohon gwamnan jihar Legas ya tashi zuwa kasar Burtaniya.
Jagoran jam’iyyar APC na kasa ya ce tafiyar tasa zuwa kasar Birtaniya na daga cikin dabarun yakin neman zabensa, inda ya ce yana tuntubar jama’a ne a kasar waje.
Duk da haka, ra’ayoyi mabanbanta sun ta bullowa da tafiyar Tinubu zuwa Landan, kamar yadda ‘yan Nijeriya suka yi iƙirarin cewa ya yi balaguro ne saboda dalilai na lafiya.
Tun kafin tafiyar tasa, Tinubu ya ziyarci wasu sassan Najeriya kamar jihohin Oyo, Neja, da Zamfara a wani bangare na tuntubar al’uma.