Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, kan rayukan da aka rasa a lokacin da wani bene mai hawa uku ya ruguje a kasuwar Kanti Kwari da ke birnin jihar.
Tinubu a cikin wata wasika ta sirri da ya rubuta wa Gwamna Ganduje mai dauke da kwanan wata 31 ga watan Agusta, 2022 ya bayyana matukar bakin ciki da juyayinsa kan wannan mummunan lamari mara dadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: Kotu Ta Wanke Tsohon Gwamns Jang Daga Zargin Almundahanar Biliyan 6.3
Ya kuma yi fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.
“Rushewar ginin bene mai hawa uku da ake ginawa abin takaici ne. Wadanda suka rasa rayukansu a wannan lamarin ba su cancanci mutuwa ta haka ba.”
“A yayin da nake addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya hutar da rayukansu, ina jajantawa iyalansu da danginsu. Ina kira gare su da su yarda da faruwar lamarin a matsayin iznin Allah.”
“Ina kuma jajantawa wadanda suka jikkata kuma ina fatan samun saukin su cikin gaggawa. Ina kira ga gwamnati da ta ci gaba da tabbatar da cewa an kula da wadanda suka jikkata yadda ya kamata.”
“Ya kamata a kara kaimi wajen ceto har sai an ceto duk wadanda suka makale a cikin ginin da ya ruguje.”
“Ina kuma yin amfani da wannan kafar domin jajanta wa shugaban kasuwar da masu gudanar da kasuwar, da ’yan kasuwar kan hatsarin da kuma asarar da aka yi.”
“A yayin da nake kira ga gwamnati da ta gaggauta bincikar al’amuran da suka haddasa rugujewar ginin don hana sake afkuwar irin haka a nan gaba, ina addu’ar da kada wannan abin bakin ciki ya sake faruwa.”
A wani labarin kuma, Ambaliyar Ruwa: Hukumar SEMA Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane Bakwai A Jihar Neja
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, NSEMA, ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai a kananan hukumomin Magama da Rafi na jihar sakamakon ambaliyar ruwa.
Babban Daraktan NSEMA, Mal. Ahmed Ibrahim Inga ne ya bayyana haka a Minna, ya kuma ce an samu mutuwar mutane shida a Magama, daya kuma a Rafi.