Tinubu ya Karɓe da Ofishin Yaƙin Neman Zaɓen Buhari na Abuja
Ofishin Gangamin yaƙin neman Zaɓe na Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da aka buɗe domin yaƙin neman Zaɓen sa a Shekarar 2019, an bada shi ga Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Ofishin dai an bada shi ga Ɗan Takarar, kwanaki kaɗan bayan Tinubu ya kada Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, da Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, da sauran ƴan Takarar Shugaban Ƙasa guda 12, a babban taron Jam’iyyar daya wakana a Eagle Square.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwastam Sun kama kayayyakin da Darajar su takai Naira Miliyan 38.5 a Katsina
Wannan cigaba dai, Ɗan Majalisar Wakilai kuma Shugaban Ƙungiyar Goyon Bayan Tinubu James Faleke ya sanar da hakan.
Faleke, wanda shine wakilin Tinubu a Zaɓen Fidda Gwani na APC, ya bayyana cewar ofishin yaƙin neman Zaɓen dake Cibiyar Kasuwanci ta Abuja, yana ɗauke da dukkanin kayayyakin sadarwa na Fasaha na zamani, da wurin kira da sauran su.
Ɗan Majalisar ya bayyana ofishin da aka bada yanzu ya koma na ofishin Hedikwatar gangamin yaƙin neman Zaɓen Tinubu.
Ofishin Yaƙin Neman Zaɓen Buhari shine wuri na biyu da aka baiwa Tinubu gudunmuwar sa.
Gwamnan Jahar Kogi Yahaya Bello shima ya bada ofishin Yaƙin Neman Zaɓen sa na Shugaban Ƙasa ga Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC Tinubu
Comments 1