Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran fadar shugaban kasa Abiodun Oladunjoye ya sanyawa hannu, a Juma’ar nan tare da rabata ga manema labarai.
KU KARANTA: An Bukaci Masoyan Lionel Messi Kowa ya Biya Dala 680 Domin Arba Da Shi A China
Tinubu ya kuma nada tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa Sanata Ibrahim Hassan Hadejia a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa.
Tinubu ya sanar da nadin tsohon gwamnan jihar Benue kuma tsohon ministan ayyuka na musamman a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari Geoge Akume a matsayin sakataran gwamnatin tarayya.
Wannan dai wani bangare ne na shirye shiryen da Bola Tinubu ke yi, domin samar da mataimakan da zasu dafa masa wajen gudanar da mulkin Najeriya na shekaru 4 nan gaba.
A wani labarin kuma: Gwamnan Zamfara Ya Musanta Cewa Yana Da Kadarorin Tiriliyan 9
Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ce bai bayyana tsabar kudi da jari, da kadarorin Naira tiriliyan 9 ba.
Gwamna Lawal Dare ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da yake tattaunawa da Rediyon Faransa RFI Hausa.
Ya ce al’ummar Zamfara ba za su fuskanci kalubale mai yawa ba idan yana da Naira tiriliyan 9, ya ce da ya yi amfani da kudin wajen ci gaban jihar.