Jigon jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ya mika fom din tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar.
Tinubu ya mika fom din ga jam’iyyar ne a ranar Laraba a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ne ya wakilceshi, tare da Dan majalisar wakilai daga mazabar Ikeja, James Faleke; tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal; tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Nuhu Ribadu, da dai sauransu.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, Tinubu ya samu rakiyar wakilai 370 daga sassan kasar nan domin mika fom din nasa na shugaban kasa.
A baya dai an ruwaito cewa a matsayin wani sharadi na gabatar da fom din tsayawa takara, jam’iyya mai mulki ta umarci ‘yan takararta na shugaban kasa su mika fom din dauke da sa hannun wakilai 10 daga kowace jiha da kuma babban birnin tarayya Abuja
Wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya da ya ga fom din, ya lura cewa, ana bukatar kowane mai neman takara ya samu sa hannun wakilai 370 da suka kunshi jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya.
Rahotanni sun bayyana cewa Tinubu ne ya fara mika fom din takararsa na shugaban kasa a tsakanin mutane 28 da ke neman tsayawa takara a jam’iyyar APC.
Wadanda Suka sayi fom din sun hada daSu ne: Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo; karamin ministan ilimi, Emeka Nwajuiba; Faston Legas, Tunde Bakare, Gwamna Mohammed Badaru na Jihar Jigawa; takwaransa na jihar Ebonyi, Dave Umahi; Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi; tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha; ministan harkokin kula da Neja Delta, Godswill Akpabio; Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, Ms Unu Onaneye, mace daya tilo da kuma Nicholas Felix.
Sauran sun hada da Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Rivers ; tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole; Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti; ministan kwadago da samar da ayyuka, Chris Ngige; tsohon Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun; tsohon kakakin, Dimeji Bankole; da Shugaban Majalisar Dattawa Ken Nnamani; Ministan Kimiyya da Fasaha, Onu; da Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva; da kuma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan