By Abbas Yakubu Yaura
Jagoran jam’iyyar (APC) na kasa, Bola Tinubu, ya tsunduma cikin rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar reshen jihar Kano domin sasanci
Tinubu wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne a ranar Lahadi ya gayyaci tsohon gwamnan jihar Kano, malam Ibrahim Shekarau zuwa Legas da nufin magance rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar ta kano.
Jagoran na jam’iyyar APC ya kuma gayyaci Abdullahi Ganduje amma gwamnan bai samu halartar zuwa taron ba saboda yana kasar wanje lokacin da aka bukaci zuwan nasa, duk da a na sa ran zai gana da Tinubu idan ya dawo daga tafiyar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Shekarau ya kasance yana jagorantar wani bangare na jam’iyyar waɗanda suka yi tawaye ga shugabannin APC a jihar waɗanda hedkwatar jam’iyyar ta kasa ta amince da su, kuma masu biyayya ga Gwamna Ganduje.
Rahotanni sun bayyana cewa Ganduje amintaccen aminin Tinubu ne wanda kuma ya nuna matukar sha’awar sa ta tsayawa takara a Jam’iyyar APC.
Shekarau wanda ke jagorantar wani bangare na jam’iyyar da hedkwatar APC ta kasa ta ƙi amince wa da su, yana ganawa da Tinubu kwana guda bayan da wasu gwamnonin APC guda biyu suka yi jawabi ga Ahmadu Danzago, shugaban bangaren Shekarau na APC a matsayin shugaban jam’iyyar a Kano, lamarin da aka yi imanin cewa an yi shi ne domin a kara rura wutar rikicin jam’iyyar a jihar.
Duk da cewa ba a samu cikakken bayanin ganawar da Tinubu da Shekarau suka yi ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ana kyautata zaton Tinubu zai yi galaba a kan Shekarau ya ba Ganduje cikakken goyon baya a matsayinsa na jagoran APC a Kano.