Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023, Sen. Bola Tinubu, a hukumance ya bayyana tsohon gwamnan Borno Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a yau Lahadi yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, dake jihar Katsina, mahaifar Buhari.
Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC yaje Daura ne domin yiwa Buhari gaisuwar Sallah tare da bayyana masa hukuncin da ya yanke na zaben Shettima a matsayin mataimakinsa.
A ranar Asabar ne Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa Tinubu ya amince da tikitin takarar Musulmi da Musulmi.
Tuni dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Alhaji Ibrahim Masari a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar din da ta gabata ya bayyana ajiye muƙamin da aka bashi a baya na kujerar mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Ya ce matakin nasa ya biyo bayan wata muhimmiyar tattaunawa da ya yi da dattijon jam’iyyar APC, Bola Tinubu.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Wannan shi ne don sanar da masu girma shugabannin jam’iyyarmu a karkashin shugaba Muhammadu Buhari, jiga-jigan ‘yan jam’iyyar da kuma al’ummar Nijeriya, sakamakon wata muhimmiyar tattaunawa da na yi da mai rike da tutar mu mai girma.
Masari ya ci gaba da bayyana cewa tuni ya mika takardar janyewa daga matsayinsa na dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Bola TInubu a zabe mai zuwa.
“Ina so in tabbatar da cewa na mika takardar janyewa da kuma takardar shaida a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.
“A madadina da na iyalai, ina mika godiya ga Asiwaju Tinubu – Shugaban kasa mai jiran gado, Insha Allahu – bisa amincewar da ya yi min kuma mun yi alkawarin ci gaba da jajircewa wajen goyon bayansa da jam’iyyar.”