Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin Bola Tinubu, Jigon jam’iyyar APC a Aso Rock a ranar Lahadi.
Sun gudanar da tarontaron ne ta hanyar sirri.

KARANTA WANNAN LABARIN: Kasashen G20 sun amince da mafi ƙarancin haraji ga manyan kamfunan kasa da kasa
A ƙarshen taron, Tinubu yace yazo ne fadar shugaban ƙasa domin ya godema Shugaban Najeriya akan ziyartar shi da yayi a Landan, inda yaje neman lafiyar sa.
“Nazo ne domin in godema Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari daya ziyarce ni a Landan a lokacin da aka yi man tiyatar gwuiwa. Ya nuna jimami, da tausayi, gaskiya Shugaba ne na daban,” inji shi.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar Shugaba Buhari ya ziyarci Tinubu a Landan a watan Ogusta.
Ga hotunan ziyarar