Tinubu Yafi Kowane Ɗan Takara Sauƙin Talla Saboda Irin Ƙudirorin sa – Keyamo
Karamin Ministan Kwadago da Aiki Festus Keyamo, ya bayyana Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki a zaben shugaban kasa na 2023, Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya fi kowa saukin sayarwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Bindiga Sun Hallaka Ƴan Sanda 4, Sun Ƙone Motoci Bayan Sun Tarwatsa Ofishin Ƴan Sanda A Imo
Keyamo, wanda aka nada Mai Magana da Yawun Ƙungiyar Yakin Neman Zaɓen shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a Shirin Siyasar mu a Yau.
Da aka tambaye shi ko nadin nasa a matsayin kakakin Ɗan Takarar shugaban Jam’iyyar abu ne mai wahala, sai ya ce, “To ya danganta da yanayin da kuka duba. Zai iya zama da wahala idan ka kalle shi daga mummunan gefen da wasu masu zagi ke kallo, musamman jam’iyyun adawa. Amma ba shakka aiki ne mai sauƙi.
“Asiwaju Bola Ahmed Tinubu shi ne Ɗan Takara mafi sauki da zai sayar da shi domin bayan duk surutu, abin ya shafi bayanai ne; bayan duk surutu shine abin da kuka yi. Za mu sanya shi a kan tebur. Muna alfahari da abinda yayi; ya samu nasara a lokacin da yake riƙe da muƙamin Gwamnati. Muna alfahari da gaske kuma babu wanda ko kusa yana da tarihin Asiwaju a ofishin gwamnati a cikin shekaru 23 ko 21 da suka gabata a Najeriya. Shi ne wanda ya fi kowa saukin sayarwa kuma za mu sayar da shi.”
Keyamo ya bayar da hujjar cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba a gwada shi ba, kuma ba a amince da shi ba, yana mai cewa Peter Obi ma yana gaban Atiku wajen yanke hukunci.
Ya ce, “Asiwaju yana da karfin faɗa aji. Babban abokin hamayyar da muke da shi a yau bai rike wani mukamin zartarwa ba inda ya bada wani umarni. Don haka ba za mu iya yin tunani na biyu ba. Atiku Abubakar bai rike wani mukami na gwamnati ba inda ya bada umarni na ƙarshe.
“Ba shi ne shugaban zartarwa ba; bai taba zama gwamna ba. Hatta Peter Obi ya sha gaban Atiku Abubakar wajen iya yanke hukunci. To ta yaya za mu miƙa kasar ga wanda bai taba sanin aiki ba. Atiku Abubakar ba a gwada shi ba, kuma ba a amince da shi ba.”