Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, zai mulki Najeriya na tsawon shekaru takwas. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma ce babu wani dalili da zai sa a kwatanta dan takarar shugaban kasan da na jam’iyyar Labour, Peter Obi.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Sowore ya Ƙalubalanci Tinubu, Atiku Kan Mahawara
Gwamna Sule ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels TV a cikin wani shirin siyasa mai suna Politics Today.
Ya ce, “Tattalin arzikin Legas ya fi na Anambra kyau a yau. E ko a’a? Samun su kamar yini ne da dare. Kun san babu kwatance.
Sai dai gwamnan ya ce man da Najeriya ke hakowa zai karu kafin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar karagar mulki.
Ya ce, “A yau duk matsalolin da muke fuskanta, muna fitar da ganga miliyan 1.2 zuwa 1.3 a kowace rana. A lokacin da Muhammadu Buhari ya mika wa Asiwaju, zai kasance ganga miliyan 1.5 a kowace rana.
“Za ku ga abin da ke faruwa a kasar nan. Tashin farashi zai karu sosai ɗaya da yardar Allah kuma duk sauran lambobi za su kau. Tinubu zai yi mulkin kasar nan na tsawon shekaru takwas da yardar Allah.”
A wani labari kuma, Shugaba Buhari Zai Halarci Taron AU A Kasar Jamhuriyar Nijar Ranar
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis zai fara wata ziyarar aiki zuwa birnin Yamai fadar mulkin Jamhuriyar Nijar domin halartar taron kungiyar Tarayyar Afirka kan bunkasa masana’antu da habaka tattalin arziki, da kuma wani zama na musamman kan ciniki cikin ‘yanci na nahiyar yankin Afirka.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis zai fara wata ziyarar aiki a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, kamar yadda mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya bayyana a wata sanarwa a ranar Larabar nan