Wani bidiyo ya da aka ɗauka ya nuna yadda mutane suka cika da mamaki bayan ganin wani fasto mai wa’azi ɗauke da kororon roba.
Faston wanda yake iƙirarin cewa shi mutumin ƙwarai ne, ya nemi mutanen dake kan layin cirar kuɗi a ATM su bari ya fara cire kuɗi duk da akwai waɗanda suka riga shi. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Matawalle Ya Ba Da Umarnin Kama Wadanda Suka Ki Amsan Tsofaffin Kudi
Ya sanya baƙar kwat sannan yana riƙe da littafi mai tsarki na addinin kirista a hannun sa. Sai dai babu wanda ya yarda da buƙatar da yazo da ita, inda wata mata take ce masa itama matar aure.
Bayan ya jira na wani ɗan lokaci sai faston ya ciro wani ƙyalle domin goge gumin da yayi a fuskar sa, kawai sai ga tulin kororon roba sun faɗo.
Sai ya duƙa yana ɗaukar su ɗaya bayan ɗaya yayin da mutane suke ta masa shaguɓe. Sai dai wani matashi ya taimaka masa wajen kwashe kororon roban da ya faɗo.
Bayan ya gama kwashe kayan sa, sai faston ya sulale ya bar wajen cikin jin kunya, yayin da mutane ke ta mamaki kan abinda ya faru.
Dabarar Da Na Yiwa Malamin Da Yake Son Yayi Lalata Da Ni -Wata Ɗaliba
A wani labarin na daban kuma, wata ɗaliba ta bayyana wata dabara da ta yiwa malamin da yake so yayi lalata da ita.
Wata budurwa wacce lakcaranta yake ƙoƙarin yin baɗala da ita tayi wata dabara domin kauce masa.
A wani bidiyo da ta sanya budurwar ta bayyana cewa sai da tayi ƙaryar cewa tana da aure domin kaucewa abinda lakcaran yake so yayi da ita.